Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA :Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, farashin danyen man Texas ya karu da kashi 0.6% a yau Laraba, inda ya kai dala 68.78%, a kan kowace ganga guda, bayan da a jiya Talata farashin ya fadi da kashi 1.4%.
Sai kuma farashin danyen mai na brent ya tashi da kashi 0.5% a yau Laraba, inda ya kai dala 72.03 a kan kowace ganga guda, bayan da a jiya Talata ya fadi da kashi 0.7%.
Ayyukan hakar maid a Amurka ke gudanarwa a cikin tekun Mexico na fuskantar cikas, sakamakon guguwar iska mai tsanani da take tafe ruwan sama mai karfi, wanda yasanya aiki hakar main yin tafiyar hawainiya, inda ya zuwa jiya Talata kusan kashi 79 na ayyukan hakar mai a rijiyoyin da ke tekun Mexico sun tsaya cak, wanda hakan yasa kasuwar mai ta yi asarar ganga miliyan 17.5.
342/